Majalisar dattawan Birtaniya ta amince da wani kudiri da ke neman haramta amfani da kafofin sada zumunta ga yara ‘yan ƙasa da shekaru 16, bayan an kada kuri’ar goyon baya tsakanin mambobin majalisar.
Rahoton BBC ya bayyana cewa gyaran dokar ya samu goyon bayan ‘yan majalisar daga jam’iyyun Conservative, Liberal Democrat da Crossbench, yayin da gwamnati ta ce za ta gudanar da nata shawarar jin ra’ayoyin jama’a kan yiwuwar haramcin.
A karkashin dokar, gwamnati za ta tilasta wa kamfanonin sada zumunta samar da hanyoyin tantance shekarun mutum kafin ya fara amfani da kafafensu.



