Barayin dajin da suka sace Kiristoci 166 a jihar Kaduna sun nemi N29m matsayin ‘kafin-alkalami’ kafin su fadi adadin kudin fansar da za a biya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa a ranar Lahadi 18 ga watan Janairun 2026, ‘yan bindiga sun kutsa cikin majami’u uku a yankin Kurmi Wali da ke kudancin Kaduna tare da sace masu ibadar.
Tun da fari dai gwamnatin jihar Kaduna ta musanta batun, kafin daga bisani ta tabbatar da faruwar lamarin.
A halin yanzu al’ummar yankin da aka sace mutanen sun tsinci kawunan su cikin firgici, inda da dama suka tsere daga muhallansu tare da dakatar da sauran harkoki, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.



