Wani rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya sun sha fetur din Naira tiriliyan 1.58 a bukuwan Kirsimeti.
Kamar yadda bayanai daga hukumar kula da albarkatun man fetur ta Nijeriya suka nuna, a kowace rana cikin watan Disambar 2025, ana amfani man fetur da ya haura lita miliyan 63 a kasar, wanda hakan ya sanya aka sha lita biliyan 1.97 cikin kwanaki 31.
Kamar yadda masana suka yi hasashe, yawan shan man fetur a karshen shekara na da nasaba da bukukuwa, baya ga tafiye-tafiye don kai ziyara wurare da kuma karuwar bukatar amfani da shi.



