Madugun darikar Kwankwasiyya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ba zai taba yin sulhu da akidunsa domin wata riba ta kansa ba, yana mai jaddada cewa gwagwarmayarsa ta siyasa ta dade tana wakiltar talakawan Nijeriya.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a Kano ranar Juma’a, jim kadan bayan Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da wasu shugabanni, sun fice daga NNPP.
Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a gidansa da ke Kano, inda ya ce tafiyar Kwankwasiyya ta ginu ne kan akida da manufa, ba kan kudi ko anfani na kai ba. Ya ce da a ce neman riba ce manufarsa, da tuni ya dauki wata hanya mai sauki ya bar tafiyar, amma ya tsaya tsayin daka saboda kishin talakawa da adalci.
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya kuma bukaci magoya bayansa da su fara shiri tun yanzu domin zaben 2027, yana mai gargadin cewa akwai wasu da ke kokarin rusa abin da aka gina tsawon lokaci a Kano.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, madugun ya jaddada cewa ba zai ja da baya ba wajen kare muradun jama’a, yana mai cewa burinsa shi ne yakar duk wani tsari da ke danniya ko zaluntar talakawa.



