DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan sanda sun kama sabuwar amarya kan zargin ajalin mijinta da guba a jihar Jigawa

-

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wani sabon ango a ƙauyen Gauza da ke ƙaramar hukumar Jahun, bayan da ake zargin ya rasu ne sakamakon cin abincin da amaryarsa ta dafa masa wanda aka saka masa guba.

Lamarin ya faru ne a ranar 23 ga Janairu, 2026, inda bayan cin abincin rana, ango ya kamu da rashin lafiya mai tsanani kuma aka garzaya da shi asibiti, inda daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.

Google search engine

Binciken farko ya nuna cewa ‘yan sanda sun kama matar marigayin a matsayin babbar wadda ake zargi, bayan da ta amsa laifin zuba gubar bera a cikin abincin mijinta. Ta kuma bayyana cewa ta tura ‘yar uwarta domin sayo gubar, tare da cewa an tilasta mata auren ne daga iyayenta, abin da ta ce ya janyo aikata wannan mummunan lamari.

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar ya bayar da umarnin mika lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) a Dutse domin zurfafa bincike, kafin gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu.

Rundunar ta bukaci al’umma su guji daukar doka a hannunsu, tare da amfani da hanyoyin doka wajen warware matsalolin aure da na iyali, tana kuma tabbatar da jajircewarta wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara