Akalla tsoffin ‘yan Majalisar Tarayya 17 sun nesanta kansu daga wani taro da aka shirya a karkashin kungiyar tsofaffin ‘yan majalisar tarayya (NFFL) domin goyon bayan wa’adin mulki na biyu ga Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu. Sun ce ba su halarci wani taro ba kuma ba su amince da duk wata sanarwa da aka fitar da sunansu ba, suna kiran taron da “shirin siyasa na yaudara.”
A wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar, sun zargi masu shirya taron da yin amfani da kudi da rarrashi domin kirkirar sahihanci na bogi. Sun ce ba za a iya wakiltar daruruwan tsoffin ‘yan majalisa da ‘yan tsiraru da aka tara a boye ba, tare da jaddada cewa tsoffin ‘yan majalisa ba kaya ba ne da za a saya ko a sayar.
Sun kara da cewa ya kamata gwamnati ta dogara da aiki da sakamako maimakon neman goyon baya ta taruka. A cewarsu, idan gwamnatin na ganin ta cancanci wa’adi na biyu, to ta gabatar da hujjojin tsaro, rage tsadar rayuwa, samar da ayyukan yi da daidaita tattalin arziki, domin “goyon baya ba shi ke tafiyar da kasa ba, aiki ne.”




Wannan maganar taku gaskiya ne. Domin kuwa tun daga 2015 lokacin da Jam’iyyar APC ta samu Shugabancin Nigeria babu wani abu na cigaba da suka kawo Kasar nan face Talauci da kuma Tabarbarewar Al’amura