Rundunar sojin Amurka ta ce ta na ƙara tura kayan aikin soja tare da faɗaɗa raba bayanan sirri da Nijeriya, a wani ɓangare na ƙoƙarin Amurka na ƙara haɗin gwiwa da rundunonin sojin Afirka domin fatattakar ’yan bindigar da ke addabar nahiyar.
Mataimakin kwamandan rundunar sojin Amurka a Afirka, Laftanar Janar John Brennan, wanda ya bayyana hakan yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ƙara da cewa Ma’aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) ta ci gaba da buɗe hanyoyin sadarwa da rundunonin soji a ƙasashen Sahel da ke ƙarƙashin mulkin soja, ciki har da Burkina Faso, Nijar da Mali, duk da sauye-sauyen siyasa da suka faru a yankin.
Wannan ya zo ne bayan harin da Amurka ta kaddamar a Nijeriya kan ‘yan ta’adda, lamarin da ya haifar da cece-kuce, duk da cewa gwamnatin Nijeriya ta kare matakin da cewa akwai sahalewar ta, kana kuma ta bayar da bayanan sirri ga Amurkan kafin kaddamar da harin.



