Sakataren jam’iyyar ADC a Nijeriya ya gargadi APC mai mulki cewa al’umma ne ke taka rawa wajen nasara a zabe ba gwamnoni ba.
Ra’uf Aregbesola ya bayyana haka ne a Abuja, inda ya ce zabukan 2023 na yankin Kudu maso yamma da Kudu maso Gabashin Nijeriya sun tabbatar da hakan.
Aregbesola wanda tsohon gwamnan jihar Osun ne, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa ADC a shekarar da ta gabata.
Ya kuma ja hankalin gwamnatin APC da ta tabbatar da ganin an gudanar da sahihin zabe a shekarar 2027, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.



