Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin APC mai mulki da lalata tsari da yanayin kasar, yana mai bayyana ta a matsayin jam’iyya mai mulki mafi muni da ya taba gani.
Atiku ya bayyana hakan ne a Abuja yayin kaddamar da littafin sakataren jam’iyyar hadaka ta ADC Bolaji Abdullahi mai taken ‘The Loyalist’, inda ya ce ko a zamanin mulkin soji ba a samu barna irin ta APC ba.
A cewar sa, ya ji dadin haduwar ‘yan siyasa da dama wuri guda a cikin jam’iyyarsu ta ADC, a yunkurin sabunta fatan Nijeriya kan turbar dimukradiyya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.



