Kyaftin din tawagar kwallon kafar Super Eagles ta Nijeriya Wilfred Ndidi ya rasa mahaifinsa Sunday Ndidi a wani hatsarin mota da ya auku a yau Talata.
Rahotanni sun bayyana cewa mahaifin Ndidi wanda tsohon soja ne, ya gamu da hatsarin ne a jihar Delta, inda bayan garzayawa da shi asibiti, likitoci suka tabbatar da rasuwar sa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Tuni kungiyar kwallon kafa ta Besiktas da Wilfred Ndidi ke taka wa leda a kasar Turkiyya ta aike masa da sakon jaje a shafinta na X.



