Fadar Shugaban Nijeriya ta caccaki madugun adawa Atiku Abubakar, bisa kwatanta gwamnatin Tinubu da mulkin soja, tana mai bayyana kalaman nasa a matsayin abinda basu dace ba.
Martanin ya biyo bayan furucin Atiku a wani taron ƙaddamar da littafi a Abuja a ranar Talata, inda ya bayyana gwamnatin APC a matsayin mummunar gwamnati mafi muni da ya taɓa gani cikin kusan shekaru 40 da yake a harkar siyasa, yana mai cewa ta fi ma gwamnatocin soja illa.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, mai ba Tinubu shawara kan harkokin yada Labarai Sunday Dare, ya zargi Atiku kalaman cin mutuncin ’yan Nijeriya.



