Jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce yana da tabbacin cewa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, tare da wadanda ke tare da shi, za su yi nadamar ficewa daga jam’iyyar NNPP.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne bayan da Gwamna ya koma jam’iyyar APC, lamarin da ya ce ya ba mutane da dama mamaki har da shi, ya ce a farko ma ya dauka kamar mafarki yake yi ganin yadda al’amura ke tafiya.
A ranar Litinin 26 ga Janairu, 2026, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya sheƙa zuwa APC, bayan da ya sanar da murabus dinsa daga NNPP a ranar Jumma’a 23 ga Janairu, 2026, kasa da shekaru uku da lashe zaben gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar.



