Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa Shugaba Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima za su sake lashe zaɓen 2027 tare a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Daily Nigerian ta rawaito Gwamna Sule na fadin hakan ne a ranar Asabar yayin wani taro da aka gudanar a Jos da ke jihar Filato, domin murnar sauya sheƙar Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, zuwa APC.
A cewarsa, shigar Gwamna Mutfwang APC ta kara karfin jam’iyyar a yankin Arewa ta Tsakiya, lamarin da zai ƙara mata ƙarfi a babban zaɓen 2027.



