A Jamhuriyar Nijar wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun yi ruwan bama – bamai daga nesa zuwa filin tashi da saukar jiragen saman birnin Yamai.
DW Hausa ta rawaito cewa harin ya soma ne da misalin karfe 12 na dare da ‘yan mintoci har ya zuwa kusan karfe daya na safiyar Alhamis.
Amma rahotanni sun ce tuni jami’an tsaron kasar ta Nijar cikin gaggawa suka shawo kan matsalar, inda jama’a a cikin unguwanni musamman na kewayen filin jirgin saman na Yamai suka kasance cike da rudani.



