DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An yi wa wasu magidanta hukuncin aikata masha’a a kasar Indonesia

-

Kotun shari’ar musulunci a lardin Aceh na Indonesia ta yi wa wani namiji da wata mata bulala 140 kowanne a bainar jama’a, bisa laifin shan giya da kuma lalata ba tare da aure ba.

Bulalar ta gudana ne a wani fili a ranar Alhamis, inda jama’a da dama suka hallara.

Google search engine

Matar ta suma bayan kammala hukuncin, lamarin da ya sa aka kai ta asibiti.

Shugaban ‘yan sandan Shari’a na Banda Aceh Muhammad Rizal ya ce kotun Shari’a ta yanke musu hukuncin bulala 100 kan zina da kuma 40 kan shan giya, lamarin da ake ganin na daga cikin mafi tsauraran hukunci tun bayan aiwatar da dokar Shari’a a Aceh a shekarar 2001 bayan samun ikon cin gashin kai na musamman.

Aceh ita ce kadai a Indonesia ke aiwatar da dokar Shari’a, inda haramun ne yin jima’i tsakanin marasa aure.

Jimillar mutane shida ne aka hukunta a ranar, ciki har da wani jami’in ‘yan sandan Shari’a da budurwarsa da aka kama a wani wuri na kashin kai; wanda suka sha bulala 23-23 kamar yadda rahoton AFP ya tabbatar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dan majalisar wakilan Nijeriya ya sauys sheka daga PDP zuwa ADC

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tambuwal/Kebbe a jihar Sokoto, Abdussamad Dasuki ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, inda ya koma ADC. A cikin wasiƙar...

Sanata Wamako ya raba wa marayu su 10,000 tallafin N1,000 kowane a jihar Sokoto

Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta Arewa, Aliyu Magatakarda Wamakko, ya bayar da tallafin miliyan 10, ga mutane dubu 10 da...

Mafi Shahara