DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Majalisar dattawa ta musanta ƙin amincewa da aika sakamakon zaɓe ta na’ura

-

Bangaren ’yan adawa a Majalisar Dattawan Nijeriya ya fayyace a ranar Alhamis cewa Majalisar ba ta ƙi amfani da tsarin tura sakamakon zaɓe ta na’ura ba a ci gaba da aikin gyaran dokar zaɓe, sabanin rahotannin da aka yaɗa a kafafen yaɗa labarai.

 

Google search engine

Wannan bayani ya zo ne sa’o’i ƙasa da 24 bayan Majalisar Dattawa ta fuskanci suka a ranar Laraba, biyo bayan rahotannin da ke cewa ’yan majalisar sun yi watsi da shawarar tura sakamakon zaɓe ta na’ura, tare da ƙin saka dokar hana masu sayen ƙuri’a da sauran masu aikata laifukan zaɓe shiga harkar zaɓe na tsawon shekaru 10.

 

Bayan yaɗuwar rahotannin, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ƙaryata labarin tare da jaddada cewa Majalisar ta bar tsarin tura sakamakon zaɓe ta na’ura yadda yake a ƙarƙashin dokar zaɓe ta 2022.

 

Da yake zantawa da ’yan jarida a ranar Alhamis, jagoran bangaren marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya ce sun ga dacewar yin wannan bayani ne sakamakon abin da ya kira “rashin fahimta” da ya biyo bayan zaman Majalisar na ranar Laraba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kotu ta yankewa tsohon shugaban bankin NEXIM hukuncin daurin shekaru 490

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, a yau Alhamis 5 ga Fabrairu, 2026, ta samu nasara a kotu, inda aka yanke wa...

Shugaba Tinubu ya girke sojoji a Kwara bayan harin da aka kai jihar

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ba da umarnin girke dakarun soji a Kwara bayan harin da ya hallaka mutane da dama a jihar.   Cikin wata sanarwa...

Mafi Shahara