Hukumomin ƙasar Mali sun kama tare da tsare ɗan jarida Youssouf Sissoko, bisa zargin cin mutuncin shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar, Janar Abdourahamane Tiani.
Sissoko, wanda shi ne Daraktan Jaridar Alternance a Mali, an kama shi ne a ranar Alhamis, 5 ga Fabrairu 2026, bayan jaridar tasa ta wallafa wani labari da a ciki ta caccaki Janar Tiani, tare da zarginsa da ɗora alhakin harin da ƙungiyar IS ta kai a Yamai kan Faransa, Bénin da Côte d’Ivoire.
A cikin labarin, jaridar ta kuma zargi Janar Tiani da ƙarya, tare da cewa yana ƙoƙarin mayar da ƙasar Nijar wani dakin gwaje-gwaje na siyasar guba.
Sai dai ƙungiyar ’yan jarida masu zaman kansu ta riga ta bayyana damuwarta kan kamun Sissoko, inda ta bukaci a bayar da belinsa kafin ranar 9 ga Maris 2026, ranar da ake sa ran a gurfanar da shi gaban kotu.


