Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa ba ta da wata alaƙa da batun bai wa ƴar TikTok Rahama Saidu mota da shago, wanda wani mai suna Sanin Jaman ya yi, a wani faifan bidiyo ya karade kafafen sada zumunta.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ofishin Mai Magana da yawun Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya fitar a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce, Sanin Jaman ya bayyana cewa kyautar da ya bai wa Rahama Saidu a kashin kansa ne, domin nuna godiya da yabon da take yi wa gwamnatin Ahmad Aliyu a jihar Sokoto.
Sai dai gwamnatin jihar ta jaddada cewa ba ta da hannu ko alaƙa da wannan kyauta, tare da nesanta Gwamna Ahmad Aliyu da gwamnatin jihar Sokoto daga lamarin baki ɗaya.


