Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi gargaɗin yiwuwar zanga-zangar ƙasa baki ɗaya da kuma kaurace wa zaɓe, sakamakon abin da ta kira ruɗani da saɓanin matsaya daga Majalisar Dattawa kan gyaran Dokar Zaɓe, musamman game da aika sakamakon zaɓe ta na’ura.
Kungiyar ta zargi Majalisar Dattawa da watsi da buƙatar jama’a ga tsarin zaɓe a Nijeriya, saboda kasa fayyace ko aika sakamakon zaɓe ta na’ura tilas ne ko a’a.
Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, inda ya ce kungiyar na nuna damuwa mai tsanani kan “ruɗani da bayanai masu karo da juna” da ke fitowa daga Majalisar Dattawa dangane da gyaran Dokar Zaɓe ta 2022, musamman a kan batun e-transmission.


