Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sallami Kwamishinan tsaron cikin gida da na jihar, Alhaji Ibrahim Gambo Galadima, daga mukaminsa.
Jaridar Punch ta rawaito cewa sanarwar sallamar ta fito ne ta bakin mai bai wa Gwamnan shawara kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, wanda ya bayyana cewa matakin na cikin sauyin da aka yi a Majalisar zartarwar jihar domin sake tsarawa da ƙarfafa aikin gwamnati.
A cewar sanarwar, sauyin na da nufin kawo sabbin dabaru, da tsarin shugabanci, da kuma inganta aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati a fadin jihar.



