Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Nijeriya, Yakubu Dogara, ya yi gargadin cewa Amurka na iya taka rawa mai zurfi, ba wai ta zura ido ba kawai, a zaben gama-gari na Nijeriya na shekarar 2027.
Dogara ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a gidan talabijin na Channels, inda ya ce sha’awar Amurka ta samo asali ne daga muhimmancin Nijeriya ga zaman lafiyar Afirka da kuma muradun Amurka na kasa da kasa.
Ya ce tsarin hulda tsakanin kasashe na duniya ya raunana, inda kasashe ke kara tsananta kare muradunsu.
Dogara ya ce Amurka ba za ta so Nijeriya ta durkushe ba, domin hakan na iya haifar da mummunan tasiri ga Afirka baki daya, don haka zai zama cikin muradunsu su sa ido sosai kan zaben 2027.



