Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON), Farfesa Sheikh Abdullahi Saleh Usman, ya sanar da yin murabus daga mukaminsa na Shugaba kuma Babban Darakta na hukumar, daga ranar Litinin, 9 ga Fabrairu, 2026.
A cikin wata sanarwar da ya aike wa manema labarai, Farfesa Usman ya ce murabus din nasa ya samo asali ne daga dalilai na kansa kawai, bayan yin addu’a da tuntubar iyalansa, ba tare da wata matsala ko sabani da gwamnati ko hukumar ba.
Ya ce ya mika rubutacciyar wasikar murabus dinsa ga Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa tanadin Sashe na 3(6) na Dokar Kafa Hukumar NAHCON ta 2006.
Tsohon shugaban hukumar ya nuna godiya ga Shugaban Kasa Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima bisa amincewa da goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake rike da mukamin, tare da yaba wa mambobin kwamitin gudanarwa, ma’aikatan NAHCON da sauran abokan hulda ciki har da hukumomin aikin hajji na jihohi da mahukuntan Saudiyya.
Yana mai addu’a ga maniyyatan Nijeriya da Hajji Mabrur.



