DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shehu sani ya goyi bayan Remi Tinubu kan hare-haren sama na Amurka a Sokoto

-

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya goyi bayan kalaman Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, na maraba da hare-haren sama da Amurka ta kai kan ‘yan ta’adda a Jihar Sokoto, yana mai cewa matakin ya dace.

Shehu Sani ya bayyana hakan ne a shafinsa na X a ranar Talata, inda ya ce hare-haren saman da aka kai a watan Disambar 2025 kan ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a Arewa maso Yamma abin a yaba ne, tare da kira da a kara kai irin wadannan hare-hare daga Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya.

Google search engine

Jaridar Punch ta ambato shi ya ce bai fahimci dalilin da ya sa wasu ke sukar Remi Tinubu ba, duk da munanan laifukan kisan gilla, fyade da garkuwa da ‘yan ta’addan ke aikatawa.

Hare-haren saman sun auku ne a ranar 25 ga Disambar 2025, inda rahotanni suka ce sojojin Amurka, tare da hadin gwiwar gwamnatin Nijeriya, suka kai hari kan ‘yan kungiyar IS a wasu yankuna na Sokoto da ke kusa da iyakar Nijar.

Uwargidan Shugaban Kasa ta yaba da matakin ne yayin wata ziyara da ta kai Washington DC, inda ta bayyana harin a matsayin alheri, tare da bukatar a kara hadin gwiwa tsakanin Nijeriya da Amurka a fannin tsaro da musayar bayanan sirri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan bindiga sun hallaka manoma 32 a jihar Niger

Akalla manoma 32 ne aka hallaka a hare-haren da ’yan bindiga suka kai kan al’ummomin Tugan-Makeri, Konsoko da Pissa a karamar hukumar Borgu ta Jihar...

Peter Obi ya bukaci matasa da su nuna kauna da kishin Nijeriya albarkacin ranar masoya

Tsohon ɗan takarar shugaban Nijeriya, Peter Obi, ya bukaci ’yan Nijeriya musamman matasa su yi bikin ranar masoya ta Valentine cikin nuna kishin ƙasa da...

Mafi Shahara