Jami’an ‘yansanda a jihar Adamawa sun cafke wani matashi da ake zargi da hada baki da ɓata-gari wajen yin garkuwa da mahaifinsa.
Mai magana da yawun rundunar SP Suleiman Nguroje ya tabbatar da kamen wadanda ake zargi da aikata laifin, bayan gudanar da binciken sirri da kuma hadin gwiwa da jami’an sa kai, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A cewar sa, rundunar ta dauki mataki ne bayan korafin da aka shigar gabanta na batan mutumin mai suna Alhaji Ahmadu a garin Malabu da ke karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa.
A cewar sa, duka matasa ukun da aka kama sun amsa hannu a sace shi, ciki har da dansa na cikinsa, kuma rundunar tana ci gaba da bincike don ceto wanda aka yi garkuwa da shi cikin koshin lafiya.



