Jam’iyyar ADC ta yi Allah-wadai da abin da ta kira yunƙurin kama tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, a filin jirgin sama ba tare da sammaci ba, tana mai cewa hakan na tayar da tambayoyi kan bin doka da nuna bangaranci.
A sanarwar da Sakataren Yada Labarai na Kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, jam’iyyar ta ce bai kamata doka ta zama makamin yaki da ‘yan adawa ba, duk da cewa babu wanda ya fi karfinta.
ADC ta kuma zargi gwamnatin APC ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu da nuna bambanci a yaki da cin hanci, tana mai cewa ana tsananta bincike kan masu sukar gwamnati yayin da wasu ke samun karɓuwa a jam’iyya mai mulki.
Jam’iyyar ta bukaci hukumomin tsaro su kiyaye kwarewa da kundin tsarin mulki, tare da jaddada cewa ya kamata siyasa ta gudana ta hanyar kuri’a da hujja, ba ta hanyar tsoratarwa ba.



