Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi Hukumar ICPC da nuna son zuciya bayan abin da ya kira yunƙurin kama tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, a filin jirgin sama bayan dawowarsa ƙasa.
Atiku ya bayyana a shafinsa na X cewa ya kai wa El-Rufai ziyarar goyon baya, yana mai cewa an yi yunƙurin kama shi ba tare da gabatar da sammaci ba. Ya wallafa hotunan ganawar sirri da suka yi a wani gida mai zaman kansa.
Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin tsaida El-Rufai a filin jirgin, amma daga bisani aka bar shi ya wuce bayan takaddama da ta ɓarke. Sai dai ICPC da sauran hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun zazzafar muhawara ta siyasa, bayan El-Rufai ya ƙara kusanci da jam’iyyar ADC tare da sukar gwamnatin tarayya a bainar jama’a kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.



