DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ya kamata INEC ta sake duba ranakun zaben 2027 saboda azumin Ramadan – Bashir Ahmad

-

Tsohon hadimin shugaban Nijeriya, Bashir Ahmad, ya bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sake nazarin ranakun da ta ayyana domin zaben 2027, yana mai cewa sun yi daidai da watan Ramadan wanda zai iya shafar halartar masu kada kuri’a Musulmi.

Kamar yadda aka sanar, INEC ta tsayar da 20 ga Fabrairu, 2027, domin zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Tarayya, yayin da za a yi na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi ranar 6 ga Maris, 2027.

Google search engine

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Ahmad ya ce wannan ra’ayi ne cikin girmamawa, yana mai cewa a watan Ramadan Musulmi kan fi mayar da hankali kan azumi da ibada, lamarin da ka iya rage shiga harkokin yau da kullum.

Ya kara da cewa duba da yawan Musulmi a Nijeriya, ya dace a yi la’akari da sauya lokaci domin tabbatar da cikakkiyar halartar jama’a da kuma karfafa hadin kai da shigar kowa a tsarin dimokuradiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

NNPP ta bukaci Fadar Shugaban Nijeriya ta wanke Kwankwaso daga zargin tallafa wa ta’addanci

Jam’iyyar NNPP reshen Kano ta bukaci Fadar Shugaban Nijeriya da Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA) su fito su wanke jagoranta na...

Kotu a Kano ta daure jarumar Kannywood Samha Inuwa watanni 6 a gidan gyaran hali

Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, Mai shari’a S.M. Shuaibu, ya yanke wa jarumar Kannywood, Saadatu Mohammed Inuwa wadda aka fi sani da Samha,...

Mafi Shahara