Gwamnatin Nijeriya ta sanar da shirin kafa kwalejin koyon likitanci ta soji “Armed Forces College of Medicine and Health Sciences” a matsayin wani mataki na dakile karancin likitoci da cike giɓin likitoci 340,000 a Nijeriya.
Shirin ya biyo bayan taron ministoci da suka haɗa da ministan ilimi Dr. Maruf Tunji Alausa, karamar minstar ilimi Suwaiba Ahmed, da ministan tsaro, Christopher Musa, tare da sauran masu ruwa da tsaki a fannin ilimi, lafiya da tsaro.
Kwalejin za ta zama wata hanya ta ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya na sojoji, horar da likitoci da masu jinya, masu kwarewa wajen kula da masu raunin a wajen yaki, da kuma samar da karin likitoci a fadin ƙasa.



