DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaba Tinubu ya yi kira da a zauna lafiya gabanin zaɓen Abuja, Kano da Rivers

-

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga masu kaɗa ƙuri’a, jami’an tsaro da jami’an Hukumar zaɓe Mai zaman kanta (INEC) da su gudanar da ayyukansu cikin tsari da natsuwa yayin zaɓukan da za a yi ranar Asabar a Babban Birnin Tarayya (FCT), Kano da Rivers.

A cikin wata sanarwa da mai bai wa Shugaban kasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, shugaban ya bukaci duk masu haƙƙin zaɓe su fito su kaɗa ƙuri’a ba tare da tsoro ba.

Google search engine

INEC za ta gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomi shida na FCT, da kuma zaɓukan cike gurbi a mazabun Ahoada East II da Khana II a Jihar Rivers, da Kano Municipal da Ungogo a Jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatin Nijeriya za ta kafa kwalejin koyon likitanci ta sojoji don magance karancin likitoci

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da shirin kafa kwalejin koyon likitanci ta soji "Armed Forces College of Medicine and Health Sciences" a matsayin wani mataki na...

Kotu ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami zuwa 27 ga Fabrairu

Kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage shari’ar tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami, tare da ɗansa Abdulaziz, zuwa 27 ga Fabrairu, 2026. Alƙaliyar kotun, Joyce Abdulmalik,...

Mafi Shahara