DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An samu ƙarancin fitowar masu zaɓe a zaɓen cike gurbi a Kano

-

An fara zaɓen cike gurbi na kujeru biyu a majalisar dokokin jihar Kano a safiyar Asabar, inda aka samu ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a a sa’o’in farko na zaɓen.

Zaɓen na gudana ne a rumfunan zaɓe 1,014 da ke cikin mazabu 24, biyo bayan rasuwar Aminu Sa’ad Ungogo mai wakiltar Ungogo da kuma Sarki Aliyu na mazabar Kano Municipal a watan Disamban 2025.

Google search engine

Kimanin masu rajista 535,000 ake sa ran za su halarci zaɓen. Rahotanni sun nuna cewa kayan zaɓe sun isa rumfunan zaɓe da wuri, amma jami’ai da mazauna yankuna sun nuna damuwa kan ƙarancin mahalarta, duk da fatan cewa yawan masu fitowa zai ƙaru yayin da rana ke tafiya.

Rahotanni daga sassa daban-daban na mazabun sun nuna cewa ana gudanar da zaɓen cikin lumana, ba tare da tangarda ba kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu jam’iyyun NNPP, PDP, da ADC a takardun zaɓen cike gurbi na Kano

Rahotanni daga Arise News sun nuna cewa manyan jam’iyyun adawa guda uku, NNPP, PDP, da ADC ba su bayyana a takardun zaɓe na zaben cike...

Trump ya ƙara harajin kashi 10% ga kasashen duniya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanya karin harajin kashi 10 cikin 100 kan dukkan kayayyakin da ake shigo da su cikin kasar, bayan da kotun...

Mafi Shahara