An tura babura masu kafa uku da aka fi sani da Keke NAPEP domin jigilar muhimman kayayyakin zabe na INEC zuwa rumfunan zabe a zaben kananan hukumomin Babban Birnin Tarayya (FCT).
An ga kekunan na tsaye a wasu cibiyoyin rarraba kaya, inda jami’an zabe ke tabbatar da an kulle akwatunan zabe da takardun sakamako yadda ya kamata kafin a tura su zuwa unguwanni daban-daban a fadin Abuja.
Jaridar The Nation ta ruwaito amfani da Keke NAPEP na zama hanya mai sauki kuma mai rahusa wajen kai kayan zabe zuwa matakin karshe, musamman a wuraren da manyan motoci ke fuskantar cunkoso ko matsalar shiga.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu rahotannin koke-koke masu yawa dangane da rarraba kayan zaben a FCT, duk da cewa masu sa ido na ci gaba da bibiyar yadda ake gudanar da aikin domin kauce wa jinkiri ko wata tangarda.



