Lamarin ya faru ne da yammacin ranar 17, ga watan Febarairun da muke ciki a lokacin da wata motar jigilar wani kamfani ke cikin tafiya kan hanyar da ke tsakanin Faya da Kouba Olanga ta fada tarkon wasu mutane masu dauke makamai inda nan take suka halaka direban motar.
To sai dai rahotanni na nuni da cewa kwana daya bayan hallaka direban ne wasu makusanta shi suka farwa maharan da suka halakashi, nan ne jami’an tsaro suka shiga lamarin, a yayin fafatawar su da maharan manyan jami’an tsaron Chadin hudu suka kwanta dama, sai dai a cewar majiyar tsaro su ma maharan an hallaka uku daga cikin su.
Wata majiya daga gwamnatin kasar ta ce za a kara tsaurara tsaro nan gaba a yankin da ke cikin hamada sahara wanda yake fama da hare hare a kan hanya.



