Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta zargi gwamnatin jihar da kai wa mambobinta hari abin da jam’iyyar ta ce ba su dace da ka’idojin dimokuradiyya ba.
A wata sanarwa da sakataren yada labaran NNPP na Kano, Injiniya Ibrahim Karaye, ya fitar, jam’iyyar ta ce gwamnati ta fara janye kujerun aikin Hajji da aka riga aka ware wa wasu daga cikin mambobinta, ciki har da tsofaffin kwamishinoni, masu ba da shawara da wasu shugabannin jam’iyyar.
NNPP ta ce wadannan mutane ’yan Kano ne, kuma suna da ’yancin cin irin wadannan abubuwa da gwamnati ke samarwa.
Haka kuma, jam’iyyar ta zargi gwamnati da tsangwama da tsoratar mambobinta domin mayar da motocin aiki da aka ba su a lokacin da suke kan mukamai, tana mai cewa motocin na daga cikin hakkokinsu da suka yi hidima.



