DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Tinubu ta musanta biyan kudin fansa don ceto daliban Papiri jihar Neja

-

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa zargin da ke yawo a wasu rahotannin kafafen yada labarai na duniya na cewa an biya kaso mai tsoka na kudin fansa domin ceto daliban da aka sace daga makarantar St. Mary’s a Jihar Niger, ba gaskiya ba ne, sannan rahotannin ba su da tushe.

Ministan Yada Labaran kasar Mohammed Idris, ya ce babu wasu kudin fansa da aka biya, kuma babu wani kwamandan ‘yan ta’adda da aka saki. Ministan ya jaddada cewa hukumomin tsaro sun musanta irin wadannan ikirari tun da farko.

Google search engine

Ya ambaci Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), da shugabannin Majalisar Dokoki ta Kasa, yana mai cewa duk sun fito karara sun musanta batun biyan kudin fansa.

Gwamnatin ta ce nasarar ceto daliban ba tare da asarar rai ba, sakamakon aikin leken asiri da tsare-tsaren soji ne. Ta kuma gargadi kafafen yada labarai da su rika tantance sahihancin bayanai kafin wallafawa, tana mai cewa rahotannin da ba su da tabbaci na iya karfafa gwiwar masu aikata laifi ko rage kwarin gwiwar jami’an tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara