DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar alhazan Nijeriya NAHCON ta umurci jihohi su mayar wa maniyyatan da ba a yi musu rajista ba kuɗaɗensu

-

Hukumar alhazan Nijeriya NAHCON, ta umarci hukumomin kula da aikin hajji na jihohi da su mayar wa maniyyatan da ba a kammala musu rajista ba kuɗin da suka biya domin aikin hajjin 2026, sakamakon raguwar adadin kujerun aikin hajji da kuma tsauraran ka’idojin biza daga Saudiyya.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar ta bayyana cewa raguwar kujerun aikin hajjin da aka ware wa Nijeriya, tare da gajeren wa’adin kammala biza da Saudiyya ta sanya, sun tilasta wa NAHCON daukar matakin da zai kare hakkin maniyyata da ba su samu damar kammala rajista ba.

Google search engine

NAHCON ta bukaci hukumomin jihohi da su tabbatar da anbi hanyoyin da suka dace wajen mayar da kuɗin, tare da sanar da maniyyata hanyoyin karɓar kuɗinsu ba tare da jinkiri ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar Wakilan Nijeriya ta ɗage komawar zaman majalisa zuwa 5 ga Maris

Majalisar Wakilan Nijeriya, ta ɗage komawar zaman majalisa daga Talata, 24 ga Fabrairu 2026, zuwa Alhamis, 5 ga Maris 2026. Sakataren Majalisar, Kamoru Ogunlana, ya bayyana...

Jam’iyyar APC za ta iya amincewa da Yilwatda da Ajibola Basiru a babban taron ta

Wasu rahotanni na nuni da cewa jam’iyyar APC na dab da amincewa da ci gaba da rike mukaman shugabancin jam’iyyar na ƙasa Yilwatda da sakataren...

Mafi Shahara