DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jihohin APC sun sake mara wa Tinubu baya matsayin dan takara a zaɓen 2027

-

Jam’iyyar APC a jihohi da dama ta sake bayyana goyon bayanta ga shugaba Bola Tinubu, a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2027.

Rahoton Daily Trust ya ce tarukan zaɓen shugabannin jam’iyyar da aka gudanar a jihohi da dama ranar Talata sun jaddada wannan matsaya, inda jihohi kamar Kaduna, Gombe, Kebbi, Taraba da Edo suka sabunta kiran Tinubu ya tsaya takara karo na biyu.

Google search engine

A jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani ya ce jam’iyyar za ta hada kai domin tabbatar da nasara daga matakin mazabu har sama.

Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya bukaci sabbin shugabannin APC na jihar su samar wa Tinubu akalla kuri’u miliyan biyu a 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da ziyarar ibada ta Kiristoci zuwa Isra’ila

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da dakatar da duk wata ziyara ta Kirista zuwa Isra’ila sakamakon halin tsaro a Gabas ta Tsakiya. Hukumar kula da ziyarar ibada...

Mata biyu da ke tsare a hannun ‘yan bindiga sun haihu a jihar Sokoto

Wasu mata biyu cikin mutum takwas da aka sace a kauyen Takatsaba da ke Karamar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto sun haifi jarirai namiji...

Mafi Shahara