DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jihohin APC sun sake mara wa Tinubu baya matsayin dan takara a zaɓen 2027

-

Jam’iyyar APC a jihohi da dama ta sake bayyana goyon bayanta ga shugaba Bola Tinubu, a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2027.

Rahoton Daily Trust ya ce tarukan zaɓen shugabannin jam’iyyar da aka gudanar a jihohi da dama ranar Talata sun jaddada wannan matsaya, inda jihohi kamar Kaduna, Gombe, Kebbi, Taraba da Edo suka sabunta kiran Tinubu ya tsaya takara karo na biyu.

Google search engine

A jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani ya ce jam’iyyar za ta hada kai domin tabbatar da nasara daga matakin mazabu har sama.

Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya bukaci sabbin shugabannin APC na jihar su samar wa Tinubu akalla kuri’u miliyan biyu a 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kungiyar Kare Hakkin Dan’Adam ta nemi a sauya ranar tantance ’yan sanda saboda Ramadan

Kungiyar Kare Hakkin Dan’Adam ta nemi a sauya ranar tantance ’yan sanda saboda Ramadan Kungiyar kare hakkin dan’Adam ta kasa da kasa (IHRC-RFT) ta bukaci a...

Kotu ta dage shari’ar Abubakar Malami zuwa 10 Ga Maris

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage sauraron shari’ar da ake yi wa tsohon Ministan Shari’a na Nijeriya, Abubakar Malami, da dansa Abdulaziz kan...

Mafi Shahara