Ministan noma na Nijeriya, Abubakar Kyari, ya ce farashin kayayyakin abinci a fadin kasar ya ragu zuwa kashi 50 cikin 100, sakamakon gyare-gyaren da gwamnatin shugaba Tinubu ta aiwatar.
Ministan ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da gwamnati ke yi don wayar da kan ‘yan kasa a Abuja ranar Juma’a, inda ya ce gwamnati ta bai wa batun tsaron abinci muhimmanci domin tabbatar da zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki.
A cewarsa, gwamnati na kokarin kara yawan noman cikin gida tare da rage dogaro da shigo da abinci daga kasashen waje, domin tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya na samun abinci mai gina jiki cikin sauki.



