Farashin man fetur ya kai kusan ₦1,080 kan kowace lita a wasu sassan birnin Legas, sakamakon tashin farashin mai a kasuwar duniya da rikicin da ke kara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa binciken da aka gudanar a gidajen mai da dama a Legas ranar Asabar din nan ya nuna farashin fetur, yanzu yana tsakanin ₦1,020 zuwa ₦1,080 kan kowace lita, gwargwadon wurin da tashar mai take.
Rahoton ya ce karin farashin ya biyo bayan karin kudin da matatar Dangote ta sanya wa fetur ga ‘yan kasuwa, inda aka kara shi zuwa ₦995 kan kowace lita daga ₦874 saboda tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya.



