Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya gargadi mambobin majalisar zartarwar jihar da su guji rashin aminci, takaddama a tsakaninsu da kuma fitar da sirrin gwamnati.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron majalisar zartarwar karo na 38, inda ya bukaci su hada kai domin ci gaban jihar da walwalar al’umma, yana mai cewa lokacin sabani da zargin juna ya wuce.
Ya kuma jaddada cewa wasu sauye-sauyen siyasa a jihar suka sa shi da wasu manyan shugabanni suka mara wa jam’iyyar APC baya domin samun karin hadin kai da gwamnatin tarayya.
Gwamnan ya kuma tabbatar da murabus din kwamishinoni biyar bayan sauyin siyasar, tare da taya sabbin ‘yan majalisar da suka lashe zaben cike gurbi murna, yana mai bukatar su yi aiki tukuru domin al’ummarsu.



