Akalla sanatoci tara daga jam’iyyu daban-daban sun sanar da komawarsu jam’iyyar ADC a zauren majalisar dattawan Nijeriya, lamarin da ya sake sauya fasalin siyasa a majalisar.
Daga cikin sanatocin da suka sauya sheka akwai Aminu Waziri Tambuwal (Sokoto ta Kudu), Enyinnaya Abaribe (Abia ta Kudu), Binos Yaroe (Adamawa ta Kudu), Victor Umeh (Anambra ta Tsakiya), Tony Nwoye (Anambra ta Arewa), Lawal Usman (Kaduna ta Tsakiya), Ogoshi Onawo (Nasarawa ta Kudu), Austin Akobundu (Abia ta Tsakiya) da Ireti Kingibe (FCT).
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta wasikun sauya shekar a zaman majalisar, inda wasu daga cikin sanatocin suka danganta matakin da rikice-rikicen cikin jam’iyyunsu na baya.
Akpabio ya ce sauya shekar na nuna matsalolin cikin gida a jam’iyyun adawa, yana mai cewa har yanzu jam’iyyar APC na da rinjaye a majalisar da sanatoci 87, yayin da ADC ta karu zuwa sanatoci bakwai.



