Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 1 ga Afrilu domin sake gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, kan zargin almundahanar kudin da ya kai Naira Biliyan 1.3.
Alkalin kotun, Peter Lifu, ya dage shari’ar ne bayan Lamido da ‘ya’yansa biyu, Aminu Lamido da Mustapha Lamido, ba su halarci kotu ba domin karanta musu tuhuma.
Hukumar EFCC na zargin su da safarar kudade ta hanyar kwangiloli na bogi lokacin da Lamido ke gwamnan jihar tsakanin 2007 zuwa 2015, zargin da kotun kolin Nijeriya ta ce dole a cigaba da shari’ar domin su kare kansu.



