DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Amurka za ta tura karin sojoji zuwa yankin Gabas ta Tsakiya

-

Gwamnatin Amurka na shirin tura karin sojoji da jiragen ruwan yaki zuwa yankin Gabas ta Tsakiya yayin da rikici da Iran ke kara tsananta, musamman a yankin.

TRT Afrika ta rawaito cewa ma’aikatar tsaron Amurka na duba yiwuwar tura karin jiragen yaki zuwa yankin domin tallafa wa rundunar da ke can.

Google search engine

Rahoton ya ce sakataren tsaro na Amurka, Pete Hegseth, ya amince da bukatar rundunar ta tura wani bangare na rundunar jiragen ruwa tare da rundunar United States Marine Corps, wadda yawanci ke dauke da jiragen yaki da kusan sojoji 5,000.

Rahoton ya kara da cewa jirgin yaki na ruwa USS Tripoli, wanda ke da sansani a Japan, tare da sojojin da ke cikinsa, sun riga sun nufi yankin Gabas ta Tsakiya domin karfafa rundunar Amurka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ban shirya yin yarjejeniyar sulhu da Iran don kawo karshen yakin da ake yi ba – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce har yanzu bai shirya yin wata yarjejeniya da Iran domin kawo karshen rikicin da ke kara tsananta tsakanin kasashen...

Tinubu ya kare Nijeriya daga faɗawa rikicin farashin mai da kasashen Duniya ke fama da shi – Uzodimma

Gwamnan jihar Imo State, Hope Uzodimma, ya ce shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya kare ƙasar daga mummunan rikicin farashin mai da ya addabi kasashen...

Mafi Shahara