DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sojoji sun ceto mutane 318 da aka sace tare da kama 74 da ake zargi da hannu – Hedkwatar tsaron Nijeriya

-

Rundunar tsaron Nijeriya ta bayyana cewa dakarun da ke aiki a sassa daban-daban na ƙasar sun ceto mutane 318 da aka yi garkuwa da su a watan Nuwamba, tare da kama wasu 74 da ake zargi da ta’addanci da fataucin mai da sauran laifuka.

A cewar Daraktan yada labarai na tsaro, Maj. Janar Michael Onoja, wanda ya yi jawabi an Abuja, ya ce a wannan watan kuma ’yan ta’adda 69 da iyalansu sun mika wuya a Arewa maso Gabas.

Google search engine

Hedkwatan tsaron ta ce dakarun sun kuma dakile satar mai da kimar ta kai sama da N217m, tare da rushe wuraren tace mai na bogi 16 da gano lita 201,700 na ɗanyen mai da lita 88,177 na dizal.

Onoja ya kuma yaba wa dakarun bisa ƙoƙarinsu, tare da roƙon jama’a da su ci-gaba da ba da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnan jihar Zamfara ya gabatar da kasafin kudi N861bn na 2026 ga majalisar dokokin jihar

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da kasafin kuɗi na Naira biliyan 861 na shekarar 2026 a gaban majalisar dokokin Jihar a Gusau, yana...

Shugaba Tinubu ya aika da sunan Dambazau domin tantancewa a matsayin jaakada

Shugaba Bola Tinubu ya ya aike da tsohon ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau, wanda ya taba zama shugaban sojin ƙasa, a matsayin jakada domin tantancewa...

Mafi Shahara