DCL Hausa Radio
Kaitsaye

APC ta dage sauya shekar Gwamnan Taraba zuwa Janairun 2026

-

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Taraba, Ibrahim Tukur, ya tabbatar cewa gwamnan jihar, Agbu Kefas, zai sauya sheƙa zuwa APC a hukumance a watan Janairu 2026.

Rahoton gidan talabijin na Channels ya ce an dage sauyin sheƙan da aka tsara ranar 19 ga Nuwamba saboda sace ɗalibai a Jihar Kebbi.

Google search engine

A wani taron manema labarai a Jalingo, Tukur ya ce an ɗauki matakan dakatar da wasu shugabannin ƙananan hukumomi saboda saba wa kundin tsarin jam’iyya, sannan ya nemi sulhu da mabiya maimakon zuwa kotu.

Haka kuma, an soke dakatarwar ɗan majalisar jihar Taraba, Abel Peter, da aka dakatar saboda zargin yin aiki da ya saba wa jam’iyya.

Shugaban jam’iyyar ya kuma yi watsi da ikirarin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na ɗaukar mulki a Taraba, inda ya ce APC ta riga ta karɓi fadar gwamnatin jihar kuma ba ta da niyyar janyewa.

Sabbin Labarai

‘Yan sanda sun koka da yawan yada labaran karya a Nijeriya – IGP

Shugaban 'yan sanda a Nijeriya IGP Kayode Egbetokun ya ce babu wata hukuma a Najeriya da ke fuskantar mummunan tasiri daga labaran karya kamar ‘yan...

Amurka ta fara gamsuwa da matakan Tinubu kan tsaron Nijeriya

Dan majalisar wakilan Amurka, Riley Moore, ya yaba wa gwamnatin Najeriya kan ceto yara 100 da aka sace daga St. Mary’s Private Catholic School a...

Mafi Shahara