Dan majalisar wakilan Amurka, Riley Moore, ya yaba wa gwamnatin Najeriya kan ceto yara 100 da aka sace daga St. Mary’s Private Catholic School a Papiri, karamar hukumar Agwara, Jihar Neja.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin X, Moore ya ce wannan ceton yana nuna himma ta gwamnatin Najeriya wajen magance matsalolin tsaro karkashin shugabancin Shugaba Bola Tinubu.
Dan majalisar ya kara da cewa an kafa kwamitin hadin gwiwa tsakanin Amurka da Najeriya don magance zargin tsangwamar Kiristoci a kasar.
Ziyarar Moore ta biyo bayan tattaunawar tsaro tsakanin Mai ba Shugaban Kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, da Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, a Washington a watan Nuwamba, inda aka tattauna zargin tsangwamar Kiristoci a Najeriya.



