Shugaban ‘yan sanda a Nijeriya IGP Kayode Egbetokun ya ce babu wata hukuma a Najeriya da ke fuskantar mummunan tasiri daga labaran karya kamar ‘yan sanda.
Shugaban ya fadi hakan ne a taron hulda da Jama’a da aka shirye a Abuja, inda ya ya bukaci jami’an hulda da jama’a su rika amsa kira cikin gaggawa a duk lokacin da labarai marasa tushe suka bayyana.
Ya kara da cewa jami’an su shirye suke su yi aikin sintiri, kan sahihan bayanan kai dauki, da haɗin gwiwa da jama’a da ‘yan jarida domin kare mutuncin aikin hukumar a kasa.



