Majalisar Dattawa ta gayyaci Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, da manyan masu ruwa da tsaki a bangaren sufurin jirage domin tattaunawar gaggawa bayan korafe-korafen jama’a game da tsadar tikitin jirgin sama a kasar.
Wannan matakin ya biyo bayan korafin da Sanata Buhari Abdulfatai ya gabatar, inda ya gargadi cewa hauhawar farashin jirgi na iya haifar da matsalar sufuri a fadin kasar, musamman yayin da ake shiga hutun karshen shekara.
A yayin tattaunawar, Sanata Buhari ya ce ‘yan Najeriya na kuka da tsadar jirgin cikin gida da ke kara tashi daga wata zuwa wata.
Ya bayyana cewa tikitin jirgi daga Abuja zuwa Legas yanzu ya kai tsakanin N400,000 zuwa N600,000, wanda ya sanya mutane da dama daina tafiya-tafiye ta sama.
Sanatan daga Jihar Oyo ya kara da cewa abin na kara dagule wa jama’a saboda matsalolin tsaro da wahalar tafiya a manyan hanyoyin mota.



