Shugaban Amurka Donald Trump ya shigar da kara a kotu yana neman diyya ta dala bilyan 5 (kimanin fam biliyan 3.7) kan BBC, bisa zargin yadda aka yi wa jawabinsa kwaskwarima da ya yi a ranar 6 ga Janairu, 2021 a cikin wani shirin bincike na Panorama.
A cewar takardun shari’ar da aka gabatar a jihar Florida, Trump na zargin gidan talabijin din da bata masa suna, tare da saba dokokin aiki.
BBC ta nemi afuwa ga Trump a watan da ya gabata, amma ta yi watsi da bukatarsa ta biyan diyya, tana mai jaddada cewa babu wani sahihin dalili na shigar da kara kan bata suna.
Lauyoyin Trump sun zargi BBC da gurbata jawabinsa da gangan, cikin mugunta da yaudara, domin bata masa suna. Har zuwa yanzu, BBC ba ta fitar da martani kan karar da aka shigar a kotu ba.



