Ministan Kuɗi kuma na Nijeriya, Wale Edun, ya saɓa wa furucin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce gwamnatin tarayya ba ta kai burin kudaden shiga na 2025 ba.
Edun ya bayyana cewa zuwa yanzu gwamnati ta samu naira tiriliyan 10.7, ne kacal daga cikin naira tiriliyan 40.8 da aka yi hasashen samu a shekarar 2025.
Tun da farko, Tinubu ya shaida wa jama’a cewa Najeriya ta kai burin kudaden shiga na 2025 tun watan Agusta, tare da jaddada cewa gwamnati ba za ta ƙara dogaro da rancen kuɗi wajen aiwatar da kasafin kuɗi ba.
Sai dai bayanin Edun ya nuna cewa akwai gagarumin gibi a kudaden shiga na bana, lamarin da ke sake tayar da hankula kan ɗorewar harkokin kuɗin gwamnatin Najeriya.



